WATAN AUGUST BA SHI KE BADA RUWA BA👈
"Watan August bashida alaƙa wajen yawaitar ruwan sama ko ƙarantarsa"
"Mutane da yawa suna da tunanin cewa watan August shine yake kawo ruwa mai yawa, ko kuma su ce an fi yin ruwa mai yawa acikinsa, wanda wannan kuma kuskure ne ƙwarai"
"Musulmi nagari baya taɓa ɗaukar wani aikin da yake haƙƙi ne na Allah ya ɗorashi akan wani ko wata halittarsa, wanda hakan kuma yana iya fitar da mutum daga cikin musulunci baki ɗaya"
"Allah shine wanda yake saukar da ruwan sama a duk lokacin da yaga dama, kuma a inda yaga dama, sabida haka watan August bashida ta'asiri wajen yawaitar ruwan sama ko ƙarantarsa, duk wanda ya ƙudurce cewa watan August shine watan ruwa, to haƙiƙa zai iya kafircewa Allah mabuwãyi"
"Watan August bashida ta'asiri ko alaƙa ta kusa ko ta nesa dangane da yawaitar ruwan sama a cikinsa, idan ma kaga anfi yin ruwa mai yawa a cikinsa, to haƙiƙa watan August ɗin ne ya daidaita da hukuncin Allah ne har takai ga ruwan sama ya yawaita a cikin wannan watan, amma ba wai don shi karan kansa watan August ɗin bane"
Comments
Post a Comment